Sale Mamman: An fi Samun Wutar Lantarki Zamanin Buhari
Ministan Wutar Lantarki a Najeriya Injiniya Saleh Mamman ya ce an samu ci gaba sosai kan yadda ake samun wutar lantarki a fadin kasar.
Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawar musamman da aka yi da shi a shirin A Fada A Cika na BBC da hadin gwiwar Gidauniyar MacArthur.
Ministan ya kalubalanci duk wanda yake da ja dangane da ikirarin nasa.
Amma ministan ya ce yanzu haka gwamnati na yunkurin ganin ta magance karancin wutar lantarki a kasar bayan gano matsalolin da ke addabar bangaren.
A cewarsa matsalar wutar lantarki al’amari ne babba, wanda ke bukatar makudan kudade da lokaci kafin a magance.
Najeriya ta dade tana fuskantar karancin wutar lantarki, wani abu da ake kallon shi ne sila na durkushewar masana’antu da dama.
Masana sun ce matsalar na hana masu zuba jari shigowa kasar domin kafa kamfanoni.
Gwamnatoci da dama sun sha yi alkawurran cewa za su kawar da matsalar karancin wutar lantarki, sai dai har yanzu babu wata gwamnatin da ta iya yin haka.
A lokacin da ya kama mulki, shugaban kasar na yanzu Muhammadu Buhari ya ce “Babu wani abu da ke matukar yin zagon kasa ga tattalin arzikin Najeriya kamar rashin wutar lantarki a tsawon shekarun nan.Ba za mu bar wannan al’amari ya ci gaba ba.”
Read Also:
Ana nan ana yin nazari domin gano hanya mafi sauri kuma mai inganci ta samar da lantarki cikin sauki ga al’ummar Najeriya.”
Sai dai ko bayan shekara biyar da hawansa kan karagar mulki, al’umma da dama na ganin cewa ba a samu wani ci gaba na a-zo-a-gani ba game da wutar lantarkin.
Wata mai sana’ar sayar da kifi da kaji da ke a garin Madalla mai suna Fatima Nurudeen ta ce “Mukan yi asara, sau da dama mukan zubar da kajinmu, da kifi saboda rashin wutar lantarki.”
Haka nan ma wani mai suna Mashkur Muhammad daga jihar Kano ya ce “Za ka ga ba a bayar da wutar yadda ya kamata, idan an kawo (Wutar lantarki) ba za ta wuce awa daya ko biyu ba an dauke.”
Shi kuma Muhammad Musa ya ce “A baya sukan kawo mana bil(Takardar biyan kudin wuta) ne na gidan baki daya amma yanzu daki-daki ake kawo bil, kuma ga shi ba mu samun wutar sosai.”
Sai dai a tattaunawar da ya yi da BBC ta awa daya a cikin shirin A FADA A CIKA, ministan wutar lantarki na Najeriya Saleh Mamman ya ce gwamnatin shugaban kasar Muhammadu Buhari ta karbi mulkin kasar nan a lokacin da karfin wautar lantarki da ake samu bai wuce megawatt 3000 ba, amma bayan kama mulkin shugaban akwai lokacin da aka iya samar da karfin wutar lantarki megawatt 5000.
Ya kuma ce al’ummar kasar sun shaida haka “Kashi 80 zuwa 90 cikin dari na ‘yan Najeriya masu samun wutar lantarki sun san cewa an samu canji.”
Sai dai ministan bai tabbatar da sahihancin wannan kididdiga tasa ba.