Sallamar Shugabannin Tsaro: Garba Shehu ya Mayarwa da Masu Batun Martani
Mataimaki na musamman ga Shugaban kasa Buhari, Malam Garba Shehu ya ce ‘yan Najeriya basu hango abinda Buhari ke hange.
Ya yi wannan zancen ne bayan da aka tambayesa dalilin da yasa shugaba Buhari ke cigaba da aiki da hafsoshin tsaro har yanzu.
Ya kara bayyana cewa mukaminsu ba mai wa’adi bane, hakkin kuma shugaban kasa ne sauya su amma ya nuna gamsuwarsa da su.
Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yada labarai, ya ce shugaban kasa bai sallami shugabannin tsaro ba ne saboda yana hango wata nagartarsu da ‘yan Najeriya basu gani.
Shehu ya sanar da hakan a wani bakuncinsa da TVC ta karba kuma jaridar Vanguard ta ruwaito.
Read Also:
A yayin martani ga tambayar da aka yi masa a kan abinda ya hana Buhari ya sallami shugabannin tsaro duk da yadda ake ta bukatar yayi hakan, Garba ya ce.
“Saboda yana ganin abinda masu caccaka basu gani. Yana ganin abinda mutane da yawa basu gani.
“Ba nadi bane mai wa’adi. Babu wata doka da tace sai shugabannin tsaro an sallamesu bayan sun kwashe shekaru biyu.
“Suna aiki ne da gamsuwar shugaban kasa. A yanzu kuwa shugaban kasan ya ce zai yi gyaran. Toh ya rage gare shi ne kawai.
Ina tunanin ya dace ‘yan Najeriya su bada uziri.” A bangaren yaki da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, Garba ya ce:
“Kasar nan tuntuni ta kasance da kalubalen rashin tsaro. Babu kasar da babu masu laifi. Kullum sauya salo kalubalen suke amma ana kokarin ganin bayansu.
“Daga abinda shugaban kasa yace, 2021 ba za ta yi wa ‘yan Boko Haram, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane dadi ba.”