Shugaba Buhari Ya Sallami Shugaban NAPTIP, Bashir Garba

 

Ministar tallafi da jin dadin jama’a ta bada shawarar sauya shugaban NAPTIP da sabuwa.

Buhari ya amince da shawarar nadin Dr Fatima don maye gurbinsa.

Garba Shehu yace Dr Fatima Waziri ta samu kwarewa daban-daban a rayuwa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami shugaban hukumar hana safarar mutane watau NAPTIP, Sanata Basheer Garba Mohammed, daga kujerarsa a ranar Laraba, 8 ga Satumba, 2021.

Buhari ya sallami Basheer ne bayan kimanin watanni hudu da nadashi.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana jawabin da ya saki da yammacin nan cewa Buhari ya maye gurbin Sanata Bashir da Fatima Waziri-Azi.

Shehu ya saki jawabin a shafinsa na Facebook.

A cewarsa, Buhari ya nada Fatima Waziri-Azi ne bisa shawarar da Ministar tallafi da walwala, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bashi.

Garba Shehu yace Buhari ya amince da sabon nadin ne saboda kokari da jajircewan da Fatima Waziri-Azi ta sami a rayuwarta.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here