Gwamnan Jahar Kogi ya Bayyana Cewa Jaharsa ta Fara Samar da Man Fetur

 

Gwamnan jahar Kogi, Yahaya Bello ya ce yanzu jahar Kogi za ta iya samar da man fetur.

Gwamnan ya fadi hakan ne bayan kammala taro da shugaba Buhari a fadar sa da ke Abuja.

Ya kuma yi alkawarin amfani da kudaden da man zai samar da cigaba da bunkasa tattalin arzikin kasa.

FCT, Abuja – Gwamna Yahaya Bello na jahar Kogi ya bayyana cewa yanzu jahar Kogi ta na samar da man fetur, Daily Trust ta rawaito.

Ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da manema labaran cikin gidan gwamnati suka yi da shi bayan ya kammala taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa da ke Abuja.

Gwamnan ya ce ya kai wa shugaban kasa ziyara ne don godiya bisa karamcin da ya yi masa da kuma yi wa mutanen sa sambarka, Daily Trust ta wallafa.

Ya yi alkawarin amfani da kudaden man wurin samar da ci gaba wurin bunkasa tattalin arzikin sauran bangarori don gudun sauran kura-kuran da kasa ta tafka a baya.

Ya bukaci shugaban kasa ya yi gaggawar kammala gyaran kamfanin Ajaokuta Steel kafin wa’adin mulkin sa ya kare.

A cewar sa:

“Na zo ne musamman don ganin mahaifina, shugaban kasa don yi masa godiya a maimakon daukacin jama’an jahar Kogi, Kogi ita ce jahar arewa ta farko da ta fara samar da man fetur.

“Mun zo don yi wa shugaban kasa godiya bisa karamcin da ya yi mana, kuma ina so in taya mutanen jahar Kogi murna da ‘yan Najeriya gaba daya. Muna rokon shugaban kasa ya taimaka ya kammala gina kamfanin Ajaokuta Steel, muna bukatar ya yi hakan kafin wa’adin sa ya kare.

“Sannan shugaban kasa ya yi farin ciki da hakan inda ya lashi takobin dawo da Ajaokuta da ranta kafin ya sauka daga mulki.

“Tunda yanzu muna samar da man fetur, ina so in tabbatar wa da jama’an jahar Kogi da ‘yan Najeriya cewa ba za mu sake maimaita kuskure da muka yi a baya ba inda Najeriya ta dogara da man fetur kadai a matsayin hanyar samar da kudin shiga.

“Duk abinda jahar Kogi za ta samar za a yi amfani da shi ne wurin bunkasa sauran bangarori, bangaren noma da dai sauran su don bunkasa tattalin arzikin kasa. Wannan hanyar ne za ta bubbugo da sauran bangarori. Ba za mu maimaita kuskuren da muka yi a baya ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here