2023: Shugaban Kungiyar Masana Kimiyyar Magunguna ta Najeriya, Mista Sam Ohuabunwa ya Bayyana Ra’ayin Fitowa Takarar Shugaban Kasa
Fitaccen masanin kimiyyar magunguna, Mista Sam Ohuabunwa, ya ce zai fito takarar shugaban kasa a 2023.
Ohuabunwa, wanda shine shugaban kungiyar masana kimiyyar magunguna ta Nigeria, PSN ya sanar da hakan ne a wata hira da aka yi da shi a talabijin.
Ya ce ba suna ya fito nema ba kawai lokaci ne ya yi da Nigeria ke bukatar sauyi na gari kuma ya gaji da bada shawara don haka zai shiga a dama da shi.
Wani fitaccen masanin kimiyyar magunguna kuma tsohon shugaban kwamitin kungiyar tattalin arziki na Nigeria, Sam Ohuabunwa ya sanar da niyyarsa na fitowa takarar shugaban kasa kasa a 2023.
Read Also:
Shine shugaban kungiyar masana kimiyyar magunguna ta Nigeria, Pharmaceutical Society of Nigeria, PSN.
“A shekaru na, ba wai zan fito domin wasa bane. Ba suna nake son yi ba … Takarar da gaske zan yi,” A cewar Mista Ohuabunwa mai shekaru 70 yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na TV360 Nigeria.
An wallafa hirar da suka yi ne a ranar Lahadi.
Mista Ohuabunwa kwararre ne da ba a san shi da shiga harkokin siyasa a Nigeria ba a baya.
Ya shaidawa wanda ke masa tambayoyin, Deji Badmus, cewa lokaci ya yi da zai shiga siyasa ya bada irin jagorancin da zai sauya kasar a maimakon ya tsaya daga baya yana bada shawarwari.
Mista Ohuabunwa ya ce ya dade yana kaucewa siyasa amma a Nigeria abubuwa har yanzu cigaba da tabarbarewa suke yi.
Ya ce yan Nigeria sun dade suna karbar kudade hannun yan siyasa kuma a halin yanzu sun gane cewa hakan ba zai haifar musu da da mai ido ba.