Daurin Auran Zahra Nasiru Bayero: Jama’a Sun Fara Sammako Zuwa Fadar Sarkin Bichi
Duk da tarin jami’an tsaron da aka girke, mutanen garin Bichi sun fara yin dafifi zuwa Fadar Sarkin garin domin halartar daurin auren ’yar Sarkin garin .
Tun da misalin karfe 6:00 na safe mutanen garin suka fara isa wajen daurin auren saboda ba sa so a basu labari.
Nan da ‘yan sa’o’i kadan za a shafa fatiha tsakanin Yusuf, dan shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gimbiya Zahra Bayero.
Kasancewar jami’an tsaro a Bichi, daya daga cikin sabbin masarautun da aka kirkiro a Kano, bai hana wasu mazauna garin da suka yi cincirindo a fadar Sarkin ba don bikin ‘yarsa.
Zahra, daya daga cikin yaran sarkin, za ta auri Yusuf, dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, a cikin ‘yan awanni kadan daga yanzu.
Read Also:
An shirya gudanar da daurin auren ne a babban masallacin Bichi.
Jaridar Daily ta ruwaito cewa a lokacin da wakilanta suka isa garin, wanda ke da tazarar kilomita 30 daga birnin Kano, wasu mazauna garin sun ce sun isa wajen tun da misalin karfe 6:00 na safe saboda ba sa son a yi wani abu babu su a taron.
Jaridar ta kuma lura da yadda aka jibge jami’an tsaro a cikin garin tare da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a kewayen babban masallacin.
An kuma ga jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya a wurare daban-daban inda motocin su da dama ke sintiri yayin da wasu manyan mutane ke isowa.
A cikin birnin na Kano, an tattaro cewa akwai jami’an ‘yan sanda da jami’an NSCDC a kusan dukkan mahada da shataletalen da suka mamaye cibiyar kasuwancin kasar.
Daya daga cikin manyan hanyoyin da aka tsaurara tsaro a cikin birnin Kano ita ce hanyar Katsina, hanya ɗaya tilo da ke zuwa garin Bichi daga birnin Kano.