An Samu Raguwar Amfani da Man Fetur a Najeriya da Kaso 30 – Mele Kyari

 

Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari ya bayyana cewa an samu raguwar amfani da man fetur a kasar da kaso 30.

Kyari ya ce wannan bai rasa nasaba da cire tallafin mai da shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi a watan Mayu da ta gabata.

Kyari ya ce an samu raguwar amfani da mai din daga lita miliyan 66.7 kafin cire tallafi zuwa lita miliyan 46 bayan cire tallafi.

FCT, Abuja – Kamfanin mai na NNPC ya nuna damuwarsa kan yadda ‘yan Najeriya su ka rage siyan mai tun bayan cire tallafin da Shugaba Tinubu ya yi.

Kamfanin ya ce an samu raguwar amfani da mai din da kaso 30 cikin dari a kasar idan aka kwatanta da watannin baya.

Meye NNPC ya ce game da man?

Shugaban kamfanin, Malam Mele Kyari shi ya bayyana haka a yau Juma’a 1 ga watan Satumba a Abuja yayin ganawa da manema labarai, PM News ta tattaro.

A ganawar tare da Kyari akwai ministan kudade da tsara tattalin arziki, Wale Edun a Abuja.

Kyari ya ce an samu raguwar shan mai din daga lita miliyan 66.7 kafin cire tallafi zuwa lita 46 bayan cire tallafi.

Kyari ya kara da cewa hakan ya nuna an samu raguwar kaso 30 daga cikin dari na amfani da mai din a kasar.

NNPC ya bayyana dalilin raguwar siyan mai din

Ya ce zuwa ranar Wednesday 30 ga watan Agusta, an samu karuwar fitar da man fetur zuwa lita miliyan 1.6.

Wannan na zuwa ne bayan samun kasa da lita miliyan daya a watannin da su ka wuce, cewar jaridar Vanguard.

NNPC ya bayyana cewa wannan raguwar bai rasa nasaba da cire tallafin mai da aka yi a kasar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com