Abinda ya yi Sanadin Mutuwar Fulani Makiyaya 28 a Nasararwa

 

Wasu Fulani makiyaya sun gamu da ajalinsu a jihar Nasarawa sakamakon tashim Bam da ya rutsa da su.

Kawo yau Alhamis, kwamishanan yan sanda ya ce mutum ashirin da takwas ne suka mutu.

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya roki Fulani kada suce zasu dau fansa kan al’umma.

Nasarawa – Akalla Fulani Makiyaya 27 suka rasa rayukansu yayinda Bam ya tashi da daren Talata a karamar hukumar Doma ta jihar Nasarawa.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Ramhan Nansel, ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Laraba a Lafia, rahoton Punch.

Nansel ya bayyana cewa Bam din ya tashi ne a garin Rukubi, iyakan jihar Nasarawa da Benue.

Ya ce hukumar na hada kai da sauran hukumomin tsaro wajen binciken abinda ya haddasa tashin Bam.

Yace:

“Da ban takaici irin wannan abun ya fari. makiyaya ashirin da bakwai suka mutu bayan tashin Bam a karamar hukumar Doma.”

“Hukumar yan sanda da abokanta na aiki tukuru domin fahimtar abinda ya faru tare da bibiyan wadanda suke da hannu ciki.”

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya lashi takobin cewa zai dauki mataki kan wadanda suka aikata wannan abin. Gwamnan ya yi kira ga Fulani makiyaya a fadin jihar su kwantar da hankulansu.

Jawabin kwamishanan yan sandan jihar Kwamishanan yan sandan jihar, Miayaki Muhammad, a jawabin da ya yiwa ChannelsTV a Lafia, birnin jihar Nasarawa.

A cewarsa:

“Sun tafi amsa Shanunsu da jami’an tsaron Benue suka kwace ne. Daga nan sai suka ji karar tashin Bam din da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.”

“A iya ilimina, kawo jiya (Laraba), mutum 27 aka bizne. Bayanin dake iso mana yanzu shine akwai wanda aka kai asibiti a Lafia kuma yanzu ya mutu.” “Labarin da muke da shi yanzu kenan, bamu da wani.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here