Yadda Wani Sanata ya Tsallake Rijiya da Baya

Sanata Ishaku Elisha Abbo ya shawo kan wani da ya taso masa da bindiga.

‘Dan Majalisar ya ci karo da wannan mutum ya na hanyar zuwa bikin aure.

Jawabin da aka fitar daga ofishin Sanatan yace har an cafke wannan tsagera.

Rahotanni sun shaida mana cewa Sanata mai wakiltar yankin Adamawa ta Arewa a majalisar dattawa, Ishaku Elisha Abbo ya tsallake rijiya da baya.

Labarin da Legit.ng ta samu daga ofishin yada labarin ‘dan majalisar shi ne ya fafata da wani mutumi da ya auka masa dauke da ‘yar karamar bindiga.

Hadimin Sanatan, Michael Volgent, shi ne ya fitar da jawabi a madadinsa, yace wannan mummunan abu ya faru ne da kimanin karfe 2:00 na tsakar dare.

Sanata Ishaku Elisha Abbo ya na hanyarsa na zuwa bikin dauren wani auren wani daga cikin ‘yanuwansa ne a garin Mubi a lokacin da abin ya faru.

Michael Volgent yace an yi yunkurin ganin bayan matashin ‘dan siyasar ne a wannan hari.

Mista Volgent ya fitar da wannan jawabi yana mai karyata rade-radin dake yawo daga wani bidiyo na cewa mai gidansa mutum ne mai saurin hannu.

Kamar yadda jawabin da Michael Volgent ya yi ya bayyana, jami’an tsaro sun yi gaba da wannan mutumi wanda ya yi wa Sanatan barazana da makami.

Abbo ya ce rashin aikin yi da talauci suke jawo irin wannan miyagun halaye a al’umma, ya sha alwashin cigaba da ba jama’a tallafi a gobe ranar Asabar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here