Sanatan LP ya Sauya Sheka Zuwa APC
Salon shugabanci da dabarun tafiyar da APC da Abdullahi Ganduje ke yi na ci gaba da jawo ra’ayin manyan ‘yan siyasa ga jam’iyyar.
A yau Talata, sanata mai wakiltar Imo ta Gabas Ezenwa Onyewuchi, ya fice daga jam’iyyar Labour tare da komawa APC.
Ana ganin wannan babban rashin da jam’iyyar Labour ta yi, zai iya kawo tangarda ga kudurin siyasar Peter Obi a zaben 2027.
Read Also:
Abuja – Sanata mai wakiltar Imo ta Gabas kuma dan jam’iyyar Labour, Ezenwa Onyewuchi, ya koma jam’iyya mai mulki a kasa ta APC.
Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ne ya karanta wasikar sauya shekar Sanata Onyewuchi a zauren majalisar a ranar Talata.
Hope Uzodimma, gwamnan Imo kuma shugaban kungiyar gwamnonin Progressives Forum (PGF) na cikin zauren lokacin da aka karanta wasikar, inji rahoton The Cable.
Sanatan na Imo ya dogara ne da sashe na 68 (1g) na kundin tsarin mulki yayin da ya yanke shawarar sauya shekararsa daga jam’iyyar Peter Obi zuwa ta Abdullahi Ganduje.