Akwai Yiwuwar Sanatocin APC 20 za su Sauya Sheka a Zaben 2023
Rahotanni daga Najeriya na cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta iya rasa rinjaye a majalisar dattawa, bayan da ake jita-jitar akalla Sanatoci 20 za su bar jam’iyyar zuwa wasu jam’iyyun adawa.
Jaridun kasar kamar Punch sun ruwaito cewa sanatocin na shirin sauya sheka ne zuwa jam’iyyun adawa na PDP, da LP, da kuma sabuwar jam’iyyar NNPP.
Kazalika wani fitaccen dan jam’iyyar kuma tsohon ministan ma’aikatar sufurin sama, Femi Kani-Kayode, ya bayyana cewa Sanatoci 22 na APC na shirin ficewa daga cikinta zuwa jam’iyyar PDP.
Read Also:
22 A ranar Laraba ne Shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu ya ce ya damu matuka kan yadda ake barin jam’iyyar.
Sanatoci bakwai ne suka sauya sheka daga APC zuwa wasu jam’iyyun, bayan sun kasa samun tikitin tsayawa takara a jam’iyyar a zaben 2023.
Daga cikinsu akwai tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau, da Yahaya Abdullahi daga jihar Kebbi, da Dauda Jika daga jihar Bauchi da kuma Ahmad Babba Kaita daga jihar Katsina.
Sauran sun hada da Lawal Yahaya Gamau daga Bauchi, sai kuma Francis Alimikhena daga jihar Edo.
Da yake magana da manema labarai bayan wata ganawar sirri da Sanatocin jam’iyyar, Mista Adamu ya ce akwai takaici irin yadda yan majalisar ke ficewa daga jam’iyyar.
Da ficewar Sanata Dauda Jika da ke wakiltar Bauchi ta Tsakiya zuwa NNPP, adadin Sanatocin APCn ya ragu zuwa 67.