Shehu Sani ya yi Ba’a ga FG Kan Neman Rancen $1.2b Daga Brazil
Shehu Sani ya yi ba’a ga gwamnatin Najeriya a kan neman rance daga kasar Brazil.
Najeriya na neman sabon rance na $1.2 biliyan na noma daga kasar ta Kudancin Amurka.
Shehu ya bayyana lamarin da cewa tamkar Ahmed Musa ne ke neman rance daga hannun Neymar Sanata Shehu Sani ya yi ba’a ga gwamnatin tarayyar Najeriya a kan shirin ranto $1.2 biliyan na noma daga kasar Brazil.
Ministar kudi, kasafi, da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed a ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba ya bayyana cewa kasar na neman kudi daga kasar ta Kudancin Amurka.
Ministar ta bayyana hakan ne a lokacin da ta gurfana domin kare kasafin kudin ma’aikatar na 2021 a gaban kwamitin majalisar wakilai kan kudi.
Read Also:
A cewarta, gwamnatin tarayya ta gabatar da bukatar ciyo bashin zuwa majalisar dokokin tarayya wanda take shirin magance matsaloli dashi a fannin noma yayinda kasar ke yunkurin mayar da shi wani hanya na samun kudaden shiga.
Ta ce gwamnati na shirin samun fili hekta 100,000 a dukkanin jihohi 36 domin noman abinci. A martaninsa, Sanata Shehu Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2015 da 2019, ya bayyana cewa neman rancen da Najeriya ke yi a wajen Brazil tamkar Ahmed Musa ke neman rance a wajen Neymar.
Musa ya kasance kyaftin a kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, yayin dan gaba na PSG Neymar ya kasance kyaftin a kungiyar Samba Boys na Brazil.
“Ahmed Musa na neman rance daga Neymar,” Shehu Sani ya wallafa a Twitter tare da kanen labarai ‘FG na neman sabon rance na $1.2bn daga Brazil.