Abinda Muka Tattauna da Tinubu a Birnin Landan – Gwamna Sanwo-Olu
Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jahar Lagos ya bayyana cewa Bola Tinubu yana cikin koshin lafiya.
Gwamnan yace sun tattaunawa abubuwa da dama da suka shafi jam’iyyar APC da kuma kasa baki ɗaya.
Sanwo Olu yace ba shi da masaniyar ranar da jigon APC zai dawo domin shi kaɗai ke da ikon yanke wa kansa.
Lagos:- Gwamnan Lagos, Babajide Sanwo Olu ya bayyana abinda suka tattauna da Bola Tinubu, jagoran APC a birnin Landan.
Dailytrust ta ruwaito manyan mutanen biyu sun gana a Landan yayin da ake jita-jitar Tinubu ba shi da lafiya kuma an kwantar da shi a asibiti.
Read Also:
Amma Gwamna Sanwo-Olu ya shaidawa manema labarai a gidan gwamnati dake Ikeja, cewa yayin ziyararsa sun tattaunawa abubuwa da dama waɗanda suka shafi APC da Tinubu.
Dagaske ne bashi da lafiya?
Gwamnan ya ƙara da cewa ya ɗauki hotuna da jigon APC ne saboda ya karyata jita-jitar dake yawo cewa an kwantar da shi a asibiti, kamar yadda the nation ta ruwaito.
Gwamnan yace:
“Kun ganshi a hotunan, kuma hoto baya ƙarya. Lafiyarsa ƙalau ba abunda ke damunsa, mun yi magana a kan abinda ke wakana a jam’iyyar mu da kuma kasa baki ɗaya.”
“Na kai masa ziyara ne domin ingani da idona, kuma domin mutane su kwantar da hankulansu babu wani abun damuwa.”
Yaushe zai dawo Najeriya ?
Da aka tambayeshi ko sun yi maganar ranar da zai dawo Najeriya, Gwamna Sanwo-Olu ya bada amsar cewa shi kaɗai ne zai iya yanke hukunci kan ranar dawowarsa.
Yace mutum shi ke da ikon yanke lokacin da zai fita kasa da kuma lokacin da ya dace ya dawo.