Dagaske Saraki Zai yi Takara da Tinubu a Zaben 2027?

 

Abuja – Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya sanar da cewa ba zai tsaya takarar shugabancin ƙasa ba a babban zaɓen shekarar 2027.

Bukola Saraki, ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da adalci a tsarin karɓa-karɓa na mulki a kasar nan.

Saraki ya janye burin takara a 2027

Tsohon shugaban majalisar dattawan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake magana a matsayin babban baƙo a shirin Politics Today na Channels TV.

Ko da yake Saraki ya amince cewa har yanzu yana da burin jagorantar Najeriya, ya bayyana cewa bayan zaɓen 2023 da ya samar da Shugaba Bola Tinubu daga kudanci, ya dace a ba wa yankin damar kammala wa’adin shekaru takwas.

Ya ce:

“A a. Ni ba zan nemi takarar shugaban kasa a 2027 ba.

“Lokacin da jam’iyyarmu ta haɗu a shekarar da ta gabata domin tattauna batun karɓa-karɓa, na goyi bayan matsayar cewa a bar shugabancin ƙasa a shiyyar Kudu a 2027.”

Dalilan Saraki na goyon bayan Kudu

Game da ko ya dace a bar wa Kudu ta karasa shekaru hudu, Saraki ya bayyana cewa wannan shi ne yarjejeniyar cikin gida da jam’iyyar PDP ta cimma wa.

Game da zaɓen 2023 kuwa, tsohon gwamnan na jihar Kwara ya bayyana cewa ya goyi bayan Atiku Abubakar ne saboda a wancan lokacin jam’iyyar ta buɗe kofarta ga kowa ya tsaya takara ba tare da nuna wani yanki ba.

Sai dai ya jaddada cewa yanayin siyasar yanzu ya canja, kuma dole ne a bi tsarin da zai tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Halin da jihar Kwara ke ciki

Baya ga batun siyasar ƙasa, Saraki ya yi magana kan yanayin mulki a jihar Kwara, inda ya nuna damuwarsa kan yadda al’ummar jihar suke cikin mawuyacin hali.

Ya bayyana cewa dawowarsa fagen siyasar jihar ba wai don yana son yin nasara ta kowace hanya ba ne, a’a, domin ya ga kura-kurai da wahalhalun da mutane ke ciki ne.

Saraki ya jaddada cewa kishin jama’ar Kwara ne ke damunsa, kuma zai ci gaba da fafutukar ganin an inganta rayuwarsu ta hanyar samar da shugabanci na gari.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here