Yadda Sarakuna Ke Haɗa Baki da Masu Aikata Laifi a Najeriya – EFCC

 

Abuja – Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) ta ce sarakuna da na hannu a aikin haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a ƙasar nan.

Hukumar EFCC ta ce duk da sarakuna sun san illar haƙar ma’aidanai ta haramtacciyar hanya, amma suna bai wa masu haƙar haɗin kai saboda za a ba su ɗan na goro.

Shugaban EFCC na ƙasa, Mr Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan a wani taro da ƙungiyar HEDA ta shirya kan cin hanci da sauyin yanayi a Abuja ranar Talata.

Daily Trust ta tattaro cewa cibiyar ‘HEDA Resource Centre’ tare da haɗin guiwar Hawkmoth da gidauniyar MacArthur ne suka shirya taron a Abuja.

EFCC ta faɗi illar haƙar ma’adanai

A rahoton Punch, shugaban EFCC na ƙasa ya ce:

“Idan muna magana kan abubuwan da ke gurɓata muhalli, dole mu ambaci haƙar ma’adabai ba bisa ƙa’ida, a shekaru biyar masu zuwa abin zai ƙara muni fiye da iillar haƙo ɗanyen mai.”

“Don haka mu sa a ran mu, wannan ne babbar matsalar, da za ku ga hotunan yadda haƙar ma’adanai ya lalata muhallai za ku sha mamaki, kuma ba ƴan kasar waje ke yi ba, mutanen mu ne.”

“Mutanen mu ne suke yin abin da zai illata muhallan da suke rayuwa a ciki, a wasu lukutan sarakuna ne ke ɗaure masu gindi.”

Olukoyede ya ɗora laifin gurɓatar muhalli a Neja Delta kama daga malalar mai da sauransu kan cin hanci da rashawa.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here