Sarakunan Gargajiya,Manyan Malaman Musulunci da na Kiristanci Sun Halarci Taron Karfafa Zaman Lafiya

Shugabannin addinin Musulunci da na Kiristanci na kokarin dinke baraka a tsakaninsu gabannin babban zaben 2023.

Sarakunan Kaduna da wasu manyan Malaman Musulunci sun halarci taron ibadah a coci don amsa gayyatar da aka yi masu na karfafa zaman lafiya.

Sun yi kira ga mabiya addinan guda biyu da su zamo masu kaunar juna sannan kada su yarda yan siyasa su raba kawunansu saboda son zuciya.

Kaduna – Gabannin babban zaben 2023, shugabannin Musulunci da sarakunan gargajiya a jihar Kaduna sun fara yunkurin karfafa hadin kai tsakanin addinai ta hanyar shiga sahun masu ibadah a cocin ECWA da ke hanyar Lemu, Kaduna a ranar Lahadi.

Shugaban kwamitin hulda da jama’a na cocin, Sanata Haruna Azee Zego, ya ce an gayyaci al’ummar Musulmi a yankin ne don su zo su yi ibadah tare cikin aminci a kokarin wanzar da zaman lafiya tsakanin addinai.

Zego ya kuma jinjinawa Musulman da aka gayyata kan amsa gayyatar zuwa cocin da suka yi, jaridar Vanguard ta rahoto.

Ya ce:

“Cocin ta gayyace mu ne a kokarinta na karfafa aminci da zaman lafiya a tsakanin addinai, ba tare da la’akari da banbancin addini ba.

“Wasu daga cikin Musulman da suka halarci taron cocin sun kasance yan Nijar da ke zama a ciki da kewayen garin da cocin yake.”

Sarakunan gargajiyan da suka halarci cocin sune Hakimin Barnawa, Alhaji Kabiru Zubairu; Wakilin Shehu Borno, Mai martaba Bata Madaki Auta, da Sarkin Dutse Alhaji Shuaibu Balarebe Abdullahi da sauransu.

Tattaunawar zaman lafiya

Daga cikin shugabannin Musulunci da suka halarci cocin da kuma yin jawabi kan zaman lafiya tsakanin addinai sune Sheikh Dahiru Abdullahi, Sheikh Dr. Hamisu Ya’u da Sheihk Shehu Ayotola.

Duk sun yarda cewa babu wani dalili da zai sa Kiristoci da Musulmi su yi fada maimakon zama masu tsaron juna, rahoton The Sun.

Sun ce:

“Ba za ka zamo Musulmi na kwarai ba idan baka kaunar makwabtanka kiristoci suma kuma haka.

“Ya kamata mu hada hannu sannan mu dawo da baya inda Kiristoci ke alaka da Musulmai tamkar yan uwansu suma kuma haka.“Musulmai da Kiristoci tagwaye ne. Kiristanci da Musulunci basu canja ba amma Kiristoci da Musulmai sun canja kuma mutane sun yi nasarar raba kan addinan biyu saboda son zuciyarsu.

“Ya zama dole mu dawo da baya inda Kiristoci da Musulmai ke kallon juna a matsayin yan uwa.”

Sheikh Dr. Ya’u, babban sakataren Masallacin Sultan Bello ya bayyana cewa:

“Shaidan shine babban matsalarmu kuma ya zama dole mu hadu don yakar shaidan.

“Ya kamata a girmama dan Adam sama da addini kuma mu yarda da juna kamar yadda muke.

“Dole mu so junanmu kuma kada mu bari yan siyasa su yi wasa da hankalinmu saboda tsarin siyasa a yanzu zai iya haifar da tarin matsaloli ga Najeriya.

“Kada mu bari yan siyasa su gwara kanmu. Ya zama dole mu hadu a matsayin tsintsiya madaurinki daya sannan mu bari yan siyasa su yi abubuwansu.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here