Sarakunan Gargajiya da Iyayen ‘Yan Bindiga Sun San Masu Kai Hare-Hare da Inda Suke ɓuya, Amma Sun ƙi Tona su – Gwamna Umahi
Gwamnan jahar Ebonyi da ke kudu maso gabashin Najeriya, David Umahi, ya yi barazanar kama iyayen ƴan awaren da ake zargi da kai hari kan fararen hula.
Gwamnan ya ce matakin zai kawo ƙarshen yawan tashin hankalin da ake yi yanzu a jahar ta Ebonyi.
Read Also:
Mista Umahi ya ce sarakunan gargajiya sun san ƴan bindigar da ke kai hare-haren da iyayen ƴan bindigar da kuma inda suke ɓuya, amma kuma sun ƙi tona su.
Yankin kudu maso gabashin Najeriya na fama da tashin hankali da ke ta ƙaruwa, wanda kuma ke da alaƙa da ƴan aware masu fafutukar kafa ƙasarsu ta Biafra.
Yayin da gwamnan na Ebonyi ke wannan barazana, gwamnatin tarayyar Najeriyar ta ce mai yuwuwa ta sanya dokar ta-ɓaci a jahar Anambra kafin zaɓen gwamnan jahar da za a yi ranar 6 ga watan Nuwamba, domin dakile tashe-tashen hankalin da ake yi a can.