Matar Mai Martaba Sarkin Orile-Kemta ta Kai Karar Shi Gaban ‘Yan Sanda Kan Damfarar ta N150m
Mai dakin Mai martaba Sarkin Orile-Kemta, Adetokunbo Tejuoso, tana karar shi.
Halima Oniru tace Mai gidan na ta ya karbi wasu kudi kimanin N150m hannunta.
Oba Ade Tejuoso ya karyata Gimbiyar, yace kudin da ya karba ba su kai haka ba.
Ogun – Halima Oniru, mai dakin Mai martaba Sarkin kasar Orile-Kemta, a garin Odeda, jahar Ogun, tana karar mai gidanta, Sarki Oba Adetokunbo Tejuoso.
Daily Trust tace Halima Oniru tana zargin Mai martaba Oba Adetokunbo Tejuoso da laifin karbar wasu kudi daga hannunta, ta hanyar yin yaudara da karya.
Wannan mata ta rubuta takarda zuwa ga shugaban ‘yan sanda na kasa, ta hannun lauyanta, J. S Agada.
Read Also:
Lauyan ya shaida wa IGP cewa Mai martaban ya nemi kudi da sunan za ayi kasuwanci ta karkashin wani kamfaninta, Haleems Integrated Services Ltd.
Oba Tejuoso:
An je gaban IGP Halima Oniru ta kuma sanar da jami’an tsaro cewa Oba Tejuoso ya karbi aron Naira miliyan 150 a hannunta, yana yi mata karyar yana neman sarauta a jahar Ogun.
A karshe Oniru ta auri Tejuoso
Oniru take cewa Basaraken ya taba nuna mata wasu takardun cinikin bogi domin ya damfare ta.
“Haka ya yi tayi mani karyar kasuwanci iri-iri, ya rika neman kudi a hannuna, har abin ya kai miliyoyi.”
“A karshe dai muka tare a matsayin mata da miji. A lokacin da muke zaman aure ne sai na fahimci asalin halinsa na damfara da aikin yaudarar mutane.”
“A dalilin haka, sai na tunkare shi, sai ya fara yi mani duka, yana barazanar zai kashe ni. A karshe ya kore ni daga gidan, ba tare da na dauki kaya na ba.”
Jaridar tace Mai martaba Oba Tejuoso ya musanya zargin, yace karya matar tayi masa, yace sam kudin da Oniru take bin shi bashi ba su kai Naira miliyan 150 ba.