‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Fadar Sarkin Kagara

 

Bayan wata daya da sako daliban Tegina, yan bindiga sun sake kai hari Neja.

Sun far wa fadar Sarkin Kagara amma an ci sa’a mai martaba ya yi tafiya.

Gwamnatin jahar ta katse layukan waya a yankin don jami’an tsaro.

Neja – Wasu tsagerun yan bindiga sun kai hari hedkwatar karamar hukumar Rafi a jahar Neja kuma sun kai farmaki fadar mai martaba Sarkin Kagara.

An ce yan bindiga sun dira fadar ne cikin babura 20 dauke da yan bindiga uku-uku.

Thisday ta rawaito cewa wani babban mai mukami a fadar ya bayyana cewa Allah ya taimaka Sarkin ba ya gari.

Yace:

“Mun yi sa’a Sarkin baya gari, ya fada min zai yi tafiya.”

An samu labarin cewa Sarkin ya tafi birnin jahar Minna domin halartan bikin yaye dalibai a makarantar New Gate College of Technology.

A yanzu dai babu labarin an kashe wani a harin saboda an katse layukan sadarwa a yankin domin taimakawa jami’an tsaro wajen aiki.

Wannan abu na faruwa ne wata daya bayan garkuwa da daliban makarantar Islamiyyan Salihu Tanko.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here