ALLAH ya yi wa Sarkin Hausawan Legas Rasuwa

 

HRH Alhaji Muhammadu San Kabir, sarkin Hausawan jihar Legas ya rasu ranar Alhamis da ta gabata.

Marigayi Kabir ya taba zama mataimaki kafin daga bisani ya zama shugaban riko a karamar Mushin ta jihar.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya taya al’ummar mutanen arewa da ke zaune Legas alhinin rashin marigayi Kabir.

Allah ya yi wa Sarkin Hausawan Legas, HRH Alhaji Muhammadu Sani Kabir, rasuwa yana da shekaru 57 a duniya.

A cikin wani takaitaccen sako da ya wallafa a shafinsa na tuwita, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya taya al’ummar mutanen arewa da ke zaune jiharsa alhinin mutuwar Sarkin.

Sanwo-Olu ya bayyana marigayi Kabir a matsayin dan gwagwarmaya wanda ya taba rike mukamin mataimakin shugaba kafin daga bisani ya zama shugaban riko a karamar Mushin.

“Ya bayar da gudunmawa mai yawa domin ganin dorewar siyasa a Nigeria.

“Ya na daga cikin ‘yan gwagwarmaya da suka yi aiki da kungiyar NADECO domin yaki da soke zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993,” a cewar Sanwo-Olu.

Kazalika, Sanwo-Olu ya yi addu’ar Allah ya ji kansa.

Marigayi Kabir ya rasu ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Disamba, 2020, sannan an yi jana’izarsa tare binne gawarsa bisa tsarin addinin Musulunci a makabartar Musulmai ta Jafojo da ke yankin karamar hukumar Agege, jihar Legas.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here