Saudiyya za ta Fara Shigar da Nama da Waken Soya Kasarta Daga Najeriya
Gwamnatin Saudiyya ta bayyana buƙatar shigar da nama ton 200,000 da kuma ton miliyan ɗaya na waken soya daga Najeriya.
Hakan na zuwa ne yayin da ƙasar ke son ƙarfafa cinikiyayya domin samun karin kudade, kamar yadda Ministan Noma na Najeriya, Abubakar Kyari, ya bayyana.
Read Also:
Ministan ya ce Najeriya na son bunƙasa hulɗar cinikayya domin samun kuɗaɗen waje musamman dala wanda zai taimaka wa ƙasar farfaɗo da darajar kudinta.
Najeriya ta daɗe tana neman rage dogaro da arzikin fetur zuwa wasu fannoni da za su taimaka wa tattalin arzikin ƙasar.
Ministan noman na Najeriya ya ce Saudiyya ta amince da buƙatar ne bayan ziyarar da Ministanta na Noma ya kawo a Najeriya.
“Kuma bayan tattaunawar, ƙasar ta aiko da buƙatarta,” a cewar Ministan.