Saudiyya ta yi Watsi da Duk Wani Yunƙuri na Kwashe Falsɗinawa daga Gaza

 

Ƙasar Saudiyya ta yi watsi da duk wani yunƙuri na kwashe Falsɗinawa daga yankinsu kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana.

Saudiyya ta ce ba za ta ƙulla duk wata alaƙa ta diflomasiyya da Isra’ila ba tare da an bai wa Falsɗinawa ƙasarsu mai ƴanci ba.

Wani mai magana da yawun ƙungiyar Hamas ya bayyana shawarar ta Donald Trump a matsayin abin takaici, wadda za ta haifar da ƙarin zaman tankiya a yankin.

Haka nan an samu wasu daga cikin sanatocin Amurka na jam’iyyar Democrats waɗanda suka soki batun, inda ɗaya daga cikinsu ya bayyana lamarin a matsayin “yunƙurin kawar da wata ƙabila daga doron ƙasa.”

Tuni Masar da Jordan suka yi watsi da batun tayin karɓar Falsɗinawan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here