Sauke Ministoci 2: Shugaban ƙasa ya ce Wannan Saukewar Somin Taɓi ne – Garba Shehu
Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke ministoci biyu na ma’aikatun Noma Sabo Nanono da kuma na Lantarki Sale Mamman.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban Najeriya, Femi Adesina ya fitar a wannan Larabar bayan taron majalisar koli.
Mista Adesina ya ce Ministan Muhalli, Mohammed Abubakar ne zai maye gurbin Ministan Noma, yayin da karamin Ministan ayyuka, Abubakar Aliyu zai maye gurbin Ministan Lantarki.
Matakin wani ɓangare ne na sauye-sauyen da shugaba Buhari ke aiwatarwa, a cewar Femi Adesina.
A shekara ta 2019 Buhari ya fitar da sunayen mutanen biyu cikin waɗanda yake son naɗawa a matsayin ministoci, kuma majalisa bayan tantacewa ta amince da naɗin nasu.
A baya dai Ministan Noma Sabo Nanono ya sha janyo ce-ce-ku-ce tsakanin al’umma musamman lokacin da ya yi batun cewa naira 30 za ta ishi mutum ya ci abinci a Kano.
Somin taɓi
Read Also:
Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan yada labarai Malam Garba Shehu a wata hira da BBC ya ce, shugaban da ya naɗa su ne ya ga cewa lokacin sauke su ya yi, “saboda haka ya sauke su ya maye gurbinsu da wasu.”
Malam Garba Shehu ya ƙara da cewa shugaban ƙasar ya ce wannan saukewar somin taɓi ne, “akwai wadanda za su biyo baya.”
“Ya ce wannan taki na farko kenan, da alama wasu na iya biyo baya,” in ji shi.
Ya ce hakan na sauke ministocin na nufin sun tafi kenan ba wai wani sabon muƙami za a ba su ba.
“Ba mu sani ba ko nan gaba zai ba su wani muamin, amma a yanzu dai Shugaba Buhari bai ce za su koma wani wajen ba.”
Sai dai Malam Shehu ya ce Shugaba Buharin bai bayyana dalilin sauke ministocin ba.
“Shi yake aiki da su, shi yake duba irin yadda suke gudanar da aikinsu ya ce ya gamsu ko bai gamsu ba. Saboda haka shi ne zai iya fadar dalilin da ya sa ya sauke su din.
“Amma mu dai a idanuwanmu ba mu ga wani laifi da suka yi ko aka yi mana bayani akai ba,” kamar yadda ya kara da cewa.