Idan ka Kwace Min Makarfafata, Ina da Sauran Tasiri Kenan a Siyasance? – Wike

 

Ministan Abuja ya yi karin haske a kan rikicin siyasar da ya dabaibaye siyasar jiharsa ta Ribas, kan yunkurin tsige Gwamna Siminalayi Fubara na jihar mai arzikin man fetur.

Da yake karbar shugabannin yankin Kudu maso Kudu a ofishinsa ranar Talata, Nyesom Wike, wanda ya kammala wa’adi biyu na mulkin jihar a matsayin gwamna, ya jaddada muhimmancin rike jihar da yake da karfi don ci gaba da samun tasiri a siyasance.

Ya nanata cewa da zarar ya rasa makarfafarsa a matsayinsa na dan siyasa, shi kenan ya rasa tasirinsa na siyasa.

Wike ya bayyana cewa babu wani kazafi da za a yi masa, wanda zai hana shi barci da minshari. A cewarsa, dole ne sai an yi abin da ya dace.

“Dukkanmu muna son kasancewa masu tasiri a fagen siyasa; dukkanmu muna son ci gaba da rike tsarinmu na siyasa,” ministan ya ce.

“Idan martabar siyasarka ce? Shin za ka bari kawai, wani ya zo ya yi jifa da kai waje? Kowa yana da makarfafarsa.

Idan ka kwace min makarfafata, ina da sauran tasiri kenan a siyasance?” Tashar talbijin ta Channels ta ruwaito cewa dangantaka tsakanin Wike da Fubara ta yi tsami sanadin barazanar da majalisar dokokin jihar suke yi ta tsige gwamnan.

Wasu sun zargi Wike da hannu a makarkashiyar tsige gwamnan. Ginin Majalisar dokokin jihar Ribas ya hargitse zuwa wani fagen dambe bayan gobara ta tashi a wani bangaren ginin a daren Lahadi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com