Sabon Nau’in Sauro da ke sa Zazzabi na Kaura Daga Asia Zuwa Afirka – Masana Kimiyya
Masana kimiyya sun ce wani mugun sauro da ke yada kwayar cutar da ke sa zazzabi, yana bazuwa zuwa Afirka daga Asiya, inda yake zama babbar barazana ga mazauna birni.
Wannan nau’in sauro wanda shi ne yake yada yawancin cutar maleriya da ake gani a biranen Indiya da Asiya, yana hayayyafa ne a cibiyoyin samar da ruwa na birane.
Read Also:
Kuma masanan sun ce wannan nau’i ne da kusan magungunan kashe sauro da ake amafani da su yanzu ba sa kashe shi.
Tuni wannan sauron ya sa an samu karuwar masu fama da cutar maleriya a Djibouti da Ethiopia, wanda hakan ya haifar da cikas ga yaki da cutar.
Masu bincike sun ce idan har ya ci gaba da yaduwa sosai a Afirka zai iya jefa rayuwar mutum miliyan 30 cikin hadari.
A nahiyar Afirka inda nan ne aka fi samun yawancin masu mutuwa a sanadiyyar cutar zazzabin sauro, galibi sauron da ke yada ta yana karkara ne.