Ga Wadanda za su Sauya Hali Kafin Sabuwar Shekara, Muna Basu Damar Yin Hakan – Janar Enenche

 

Hedkwatar tsaro ta yi jan kunne da kakkausar murya ga dukkan wasu ‘yan ta’adda da ke fadin kasar nan.

Manjo Janar John Enenche ya ce babu shakka sojin Najeriya za su sauya salon yaki da ta’addaci a kasar nan.

Ya sanar da hakan ne yayin wani taron manema labarai a Abuja a kan yadda shekarar 2021 za ta kasance wa hukumar.

A ranar Alhamis, hedkwatar tsaro ta ja kunnen ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga , masu garkuwa da mutane da duk wasu masu aikata laifi da ke sassan kasar nan da su tuba tare da gujewa aikata laifukan kafin dakarun sojin su far musu a 2021.

Shugaban fannin yada labarai na dakarun sojin, Manjo Janar John Enenche, a wani taron manema labarai a Abuja, ya ce a tudu, iska da ruwa duk sun fara sauya salon yakar ‘yan ta’adda da masu kai musu bayanai, The Nation ta ruwaito.

Ya ce, “Mayakan ta’addancin Boko Haram, ‘yan bindiga da dukkan sauran masu laifuka gara su tuba a yayin da za mu shiga 2021. Babu shakka sakon da muke da shi ga ‘yan ta’adda shine, kai tsaye kun saka hannu a tikitin mutuwarku saboda aiki ne da dole mu aiwatar.

“Kamar yadda aka karfafa mu, mun saka hannu a kan aikin kare kasarmu da ‘yan kasan baki daya. Rayuwa za ta koma daidai ta yadda tattalin arziki da sauran rayuwa za ta dawo.

“Ga wadanda za su sauya hali kafin sabuwar shekara, muna basu damar yin hakan. Har yanzu kofofi a bude suka garesu don su tuba. Su miko kansu ga jami’an tsaron da ya dace.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here