Sauya Sheka da Femi Kayode ya yi Zuwa APC Shawara ce Mai Kyau ga Jam’iyyar – Kungiyar Matasa

 

Kungiyar GYB2PYB Youth Support Group ta marabci Femi Fani-Kayode zuwa jam’iyyar APC.

Kungiyar ta bayyana zuwansa jam’iyyar alheri ne wajen sauya Najeriya ba jam’iyyar kadai ba.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa zuwansa ya kara wa jam’iyyar girma ba a Najeriya kadai ba GYB2PYB Youth Support Group ta yabawa Gwamna Yahaya Bello bisa matakan da suka dauka har zuwa yanzu don sanya APC a matsayin babbar jam’iyyar siyasa a Afirka, Vanguard News ta ruwaito.

A jiya gwamnan jahar Kogi tare da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Gwamna Mai Buni na jahar Yobe sun karbi tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Da yake maida martani, GYB2PYB a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Darakta Janar dinta a ranar Talata, Amb. Oladele John Nihi ya ce sauya sheka da ake zargin Fani-Kayode ya yi zuwa APC shawara ce mai kyau ga jam’iyyar, ya kara da cewa.

“burin cimma sabuwar Najeriya wani aiki ne na gama gari”.

Kungiyar ta ce zargin ficewar da jigon na PDP ya yi zai kawo babban canji ga ci gaban siyasar Najeriya, ta kara da cewa wannan yunkuri da tsohon Ministan ya yi.

“ba wai kawai kari bane ba, amma ya nuna karara na nuna gaskiyar jajircewar shugabannin jam’iyyar cewa APC gida ne ga kowa ”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here