PDP Zuwa APC: Sanata Odey da Magoya Bayansa Sun Sauya Sheƙa
Sanata Steven Odey, tare da dumbin magoya bayansa sun sauya sheƙa daga PDP zuwa Jam’iyyar APC mai mulki.
Sanata Odey ya shafe watanni takwas a majalisar dattijan Najeriya, kafin daga bisani kotu ta tsige shi, kuma ta maye gurbinsa da wani ɗan PDP.
Manyan jiga-jigan APC a jahar Cross River, cikinsu harda mataimakin gwamna sun halarci taron karbar sanatan.
Cross River – Sanata Steven Odey, na jam’iyyar adawa ta PDP, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki, kamar yadda The Nation ta rawaito.
Odey, wanda aka tsige daga kujerar sanata a watan da ya gabata bayan hukuncin kotu da cewa ba shi PDP ta tsayar takara a zaɓen cike gurbi ba, wanda ya gudana ranar 5 ga watan Disamba, 2020, ya koma APC tare da dubbannin masoyansa.
Read Also:
Ya sauya shekar ne a gundumarsa Yache, ƙaramar hukumar Yala a jahar Cross Rivers cikn ƙarshen makonnan.
Jiga-Jigan APC sun halarci bikin sauya shekar sanatan
Manyan masu faɗa aji na APC a jahar, da suka haɗa da mataimakin gwamna, Farfesa Ivara Ejemot Esu, wanda ya wakilci gwamna Ben Ayade.
Tsohon sanatan ya gode wa shugabannin APC Tsohon sanatan ya gode wa shugabannin jam’iyyar APC bisa kyakkyawar tarbar da suka masa cike da soyayya.
Hakanan kuma ya nuna farin cikin bisa yadda dubbannin magoya bayansa suka amince su sauya sheƙa tare da shi zuwa APC.
Meyasa ya koma APC?
Ya kuma bayyana cewa ya ɗauki matakin komawa APC ne saboda mutanensa sun bukaci ya yi hakan, yi wa jama’a aiki ba shi da alaƙa da jam’iyyar siyasa, inji shi. Yace: “Babban burina da kuma yanayin da nake gudanar da rayuwata shine na yi wa mutane aiki, kuma ba don samun wani sakamako ba.”