‘Yan Boko Haram Sun Fice Daga Sansanin su a Arewa Maso Gabas Don Hada Karfi da ‘Yan Bindiga

 

Rahotannin tsaro da muke samu daga majiyoyi daban-daban sun bayyana yadda Boko Haram ke horar da ‘yan bindiga .

A halin da ake ciki, ana zargin wasu mayakan Boko Haram na ci gaba shigowa yankunan Arewa maso yamma.

An suna kitsa yadda ake sace mutane da kai hare-hare kan mazauna daban-daban a yankunan.

Kaduna – ‘Yan Boko Haram sun fice daga sansanin su a Arewa maso Gabas don hada karfi da ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma, inda suke gudanar da horon makamai da garkuwa da mutane, kamar yadda majiyoyin sojoji suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP ranar Juma’a.

Kungiyar Boko Haram na kara neman hadin kai da kungiyoyin ta’addanci tun bayan mutuwar shugabansu Abubakar Shekau a watannin da suka gabata, inji rahoton Punch.

Kungiyar ISWAP na shiga yankunan Boko Haram, inda take yakar masu biyayya ga Shekau, lamarin da ya kai har wasu ke mika wuya ga ISWAP din ko sojojin Najeriya.

Wasu majiyoyin sojoji guda biyu sun ce wani bangare mai biyayya ga Shekau da ke jahar Borno ya tura kwamandoji biyu da mayaka 250 zuwa dajin Rijana da ke arewa maso yammacin jahar Kaduna.

Duk kwamandojin biyu suna kawance da Bakoura Buduma, wani shugaban Boko Haram wanda har yanzu yake biyayya ga Shekau kuma mayakan sa suna adawa da hadin kan ISWAP, a cewar majiyoyin tsaro.

Daya daga cikin majiyoyin sojoji ya ce “su ne suke kitsa wasu sace-sacen da ake yi a yankin Arewa maso Yamma.”

Majiyoyin biyu sun ce mayakan na Boko Haram suna kuma horar da gungun ‘yan bindiga, da aka fi sani da ‘yan fashin daji a yankin yadda za su harbo makamai masu saukar ungulu da abubuwan fashewa da sauran makamai.

Ba a iya samun jin ta bakin kakakin rundunar sojoji ba. Jami’an jahar Kaduna suma ba su mayar da martani nan take ba kan bukatar tabbatar da lamarin.

Sanarwar wata hukumar tsaro ta Najeriya a farkon wannan watan ta yi gargadin cewa wani kwamandan Boko Haram da sojojinsa na kasa na hijira daga sansanin su a jahar Borno zuwa jahar Kaduna a Arewa maso Yamma.

Manazarta sun ce akwai alamun da ke nuna cewa masu ‘yan Boko Haram da ‘yan bindigan suna habaka alaka mai zurfi inda duka biyun suka tsaya don samun hanyoyin samun makamai da aikata ta’addanci Arewa maso Yammacin Najeriya ta dade tana fama da gungun ‘yan bindiga, amma a bana, hare-hare da garkuwa da mutane sun karu.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here