Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya ta Sauya Lokutan Tashin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna

 

Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya, ta sanar da sauya lokutan tashin jiragenta guda biyu daga tashar Idu zuwa Rigasa.

Manajan sufurin jiragen kasan, mista Pascal Nnorli, shi ya tabbatar da hakan yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai ta Najeriya, NAN a yau Juma’a.

Mista Pascal ya ce daga yanzu jirgin kasa da ke tashi 3:30 daga tashar Idu a Abuja, zai koma tashiwa 3:00, inda kuma zai isa Kaduna 5:08 na yamma.

”Sannan Jirgin da ke tashi 2:00 na rana daga tashar Rigasa, a yanzu zai koma tashiwa 1:30 na rana, ya kuma isa Abuja 3:37 maimakon 4:07 na yamma.” in ji mista Pascal.

Ya ce sauyin zai fara aiki ne daga ranar 12 ga watan Disamban da muke ciki.

Mista Nnorli, ya kuma ce hukumar kula da jiragen kasan na yin duk mai yiwuwa domin kare lafiya da dukiyoyin fasinjojinta a kowane lokaci.

Kamfanin sufurin jiragen kasan ya dawo zirga-zirga ne a ranar 5 ga watan Disamba bayan kusan wata takwas da kai wa wani jirgi hari a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here