Shawo Kan Matsalar Tsaro: Sifeto Janar na ‘Yan Sanda ya Sauyawa Manyan ‘Yan Sandan Yankin Kudu Wurin Aiki

 

Usman Baba Alkali, sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya ya sauyawa manyan ‘yan sandan yankin kudu wurin aiki.

Sauyin wurin aikin ya shafin kwamishinan ‘yan sandan jahar Anambra da wasu mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda 16.

Hakan na zuwa ne yayi da ake tsaka da hargitsi tare da tarzoma a jahohin yankunan kudu maso gabas na kasar nan .

Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya sauyawa manyan jami’an ‘yan sandan yankin kudu maso gabas wurin aiki a matsayin hanyar shawo kan matsalar tsaro a yankin.

Frank Mba, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya ya sanar da wannan cigaban a wata takarda da ya fitar a ranar Juma’a, The Cable ta ruwaito.

Daga cikin wadanda aka sauyawa wurin aikin akwai Monday Bala Kuryas, kwamishinan ‘yan sanda na jahar Anambra.

Mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda 16 lamarin ya shafa kuma hakan ya gangara har zuwa jahohin kudu kudu na kasar nan.

Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here