Sanata Godswill Akpabio ya Bayyana Ce Akwai Siyasa a Game da Aika-Aikan da ‘Yan Bindiga Suke yi a Fadin Kasar nan

 

Sanata Godswill Akpabio ya na ganin akwai siyasa a sha’anin rashin tsaro.

Ministan ya bayyana wannan ne a lokacin da ziyarci Hedikwatar APC jiya.

Tsohon Gwamnan Akwa Ibom ya bukaci a binciki masu tada zaune-tsaye.

Mai girma Ministan harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio, ya furta albarkacin bakinsa a game da matsalar rashin tsaro da ake fama da ita.

Da yake magana, Godswill Akpabio ya bayyana cewa akwai burbushin siyasa a game da aika-aikan da ‘yan bindiga su ke yi a fadin kasar nan.

Daily Trust ta ce Sanata Godswill Akpabio ya yi wannan bayani a ranar Alhamis lokacin da ya zanta da ‘yan jarida da ya ziyarci hedikwatar APC.

“Ina ganin duk abubuwan da su ke faruwa su na da alaka da siyasa.” Inji Ministan na Neja-Delta. “Saboda haka dole mu yi amfani da madubin duba-rudunmu, mu gano matsalar, mu bankado wadanda su ka jefa mu cikin halin da mu ke ciki.”

Godswill Akpabio ya kara da cewa: “Abin da ya kare faruwa yanzu ba a jinin Najeriya ba ne.” Yace yanzu ba lokaci ne na jifan juna da zargi ba. “Dole mu yi duk abin da za mu iya, ko da ta shawarwari ne, mu tabbatar Najeriya ta zauna a dunkule.”

Akpabio bayyana makusudin zuwansa babban ofishin jam’iyyar APC, ya ce ya zo ne domin ya jaddada mubaya’arsa ga shugabancin Mai Mala Buni.

Tsohon gwamnan Akwa Ibom yake cewa ya ziyarci hedikwatar ne domin ya ba shugabannin rikon kwarya shawarar yadda za su tafiyar da jam’iyya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here