2008-2021: Sauyin Yanayi ya ɗaiɗaita Mutane Miliyan 6 a Najeriya – Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin tarayya ta ce sama da mutum miliyan shida ne sauyin yanayi ya ɗaiɗaita a Najeriya tsakanin shekara ta 2008 zuwa 2021.
Babban kwamishina a hukumar kula da ‘yan gudun hijira da ‘yan cirani , Imam Sulaiman-Ibrahim ne ya bayyana hakan a tattaunawa game da hijira da aka gudanar jiya a Abuja.
Read Also:
Ya bayyana cewa rahoton hukumar sa ido kan ‘yan gudun hijira, ya nuna cewa ƙasar ta fuskanci bala’o’i na sauyin yanayi 131 a tsawon wannan lokaci.
Ya kara da cewa alkaluman sun fi na yawan mutane miliyan 4 da rabi da rikice-rikice ya ɗaiɗaita.
Tun da farko a jawabinta, ministar ma’aikatar agaji da kaucewa bala’o’i, Sadiya Umar-Faruk, ta ce gwamnatin tarayya, ta nuna zimma da kuma jajircewa wajen takaita bala’o’in da sauyin yanayi ya haddasa.