Ana Fargabar Yan Cirani Sun Nutse a Teku #Senegal

A ƙalla ƴan cirani 100 ne su ka ɓata a gabar tekun Senegal kilomita 80 kafin su isa Ganga.

Lamarin ya faru ne bayan da kwale-kwalen da su ke ciki ya kama da wuta ya kuma nutse.

Rahotanni sun ce suna kan hanyar su ce ta isa tsibirin Canary da ke Sfaniya, a lokacin da ɗaya daga cikin injinan jirgin ya samu matsala.

Kuma a daidai lokacin da ma’aikatan jirgin ke kokarin gyara shi ne ya yi bindinga.

An samu raguwar kwararar ‘yan cirani a Turai
An kama mutanen da ake zargi da ƙona ɗan Najeriya a Libya
To sai dai rundunar sojin ruwan Senegal ta yi nasarar kuɓutar da mutum 59 daga cikin ƴan ciranin.

Hukumomi a Sfaniya sun kara tsaurara tsaro a yankin na Canary Island, lura da yadda yan cirani ke tururuwa yankin a kokarin su na ketarawa Tarayyar Turai.

Sama da yan cirani 1,000 ne su ka isa Canaty Islands a makonni biyun da su ka gabata, kamar yadda alkaluman kungiyar agaji ta Red Cross su ka nuna.

Kuma shi ne adadi mafi yawa tun bayan shekarar 2006, a lokacin da ƴan cirani 35,000 su ka isa yankin archipelago.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here