SERAP ta Sha Alwashin Gurfanar da Majalisar Wakilan Najeriya a Gaban Kotu
Kungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta yi barazanar gurfanar da majalisar wakilan Najeriya a gaban kotu, saboda aniyarta ta yin doka game da shafukan sada zumunta.
Read Also:
SERAP ta ce matsawar majalisar ta yi muhawara game da wannan ƙuduri, kuma ta amince da shi harma ta miƙawa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari don rattaba hannu, to kuwa ba makawa za ta amsa gayyata daga kotu.
Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, a wani martani ga gwamnonin shiyyar arewacin Najeriya da suka bayyana goyon bayansu ga majalisar domin yin doka a kan shafukan zumunta.
Ƙungiyar ta ce ƴan Najeriya na da damar bayyana ra’ayoyinsu a shafukan sada zumunta ba tare da wani ya musu shamaki ba.
”Ba zamu amince da duk wani ynƙuri ka iya dakile wannan dama da jama’a ke da ita ba” in ji SERAP.