Shahararren Malamin Islama a Jihar Kwara ya Rasu Sakamokon Ambaliyar Ruwa
Wani shahararren Malamin Islama a jihar Kwara, Sheikh Abdulganiyu Nuraini, ya rasu sakamakon Ambaliyar ruwa.
Bayanai sun nuna cewa ruwan ya yi awon gaba da motar Malamin tare da wasu ɗalibansa biyu lokacin da zaau tsallaka wata gada a Ilorin.
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya kaɗu da faruwar lamarin ya kuma jajanta wa iyalansa.
Kwara – Fitaccen Malamin addinin Musulunci a jihar Kwara, Sheikh Abdulganiyu Nuraini, wanda aka fi sani da Alfa Gani Aboto da ɗalibansa biyu Alfa Azeez Omoekun da Alfa Nurudeen sun rasu sakamakon Ambaliya ranar Asabar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar Lahadi aka samu nasarar tsamo gawarwakinsu da Motar da suke ciki bayan ruwan ya janye.
Bayanai sun nuna cewa Shehin Malamin da ɗalibansa na kan hanyar koma wa gida daga wurin Da’awah da suka halarta a Minna, jihar Neja yayin da ruwan ya yi gaba motarsa Toyota Yaris.
Read Also:
An tattaro cewa ruwan ya yi awon gaba da Motar Malamin yayin da yake kokarin tsallake wata gada kusa da Anguwar Harmony Estate/Kukende da ke yankin Akerebiata, Ilorin.
Marigayi Shekih ya kasance ɗalibin Muftin Ilorin na farko, Marigayi Sheikh Kamaldeen Al-Adabiy, kuma shi ne shugaban ƙungiyar Ansarul Islam Society of Nigeria.
Haka zalika Alfa Gani Aboto, mahaddacin Alƙur’ani ne kuma jagora wajen horas da mahaddata a jahar Kwara.
Tuni aka kai gawarsa mahaifarsa Aboto, ƙaramar hukumar Asa da ke jihar Ranar Lahadi bayan an yi masa Sallar Jana’iza a Ilorin.
Manyan mutane sun jajanta rasuwar Malamin
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, Bukola Saraki, Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Zuku Gambari, na daga cikin manyan mutanen da suka nuna kaɗuwarsu da faruwar lamarin.
Bayan haka sun yi Ta’aziyya ga iyalan marigayi Shehin Malamin da sauran waɗanda Ibtila’in ya rutsa da su.
Ambaliyar da ta auku sakamakon matsanancin ruwan sama ta lalata gadoji, wuraren kasuwanci sannan kuma ta mamaye gine-ginen gwamnati da gidajen mutane a Kwara, ya yi ajalin rayuka da dama.