Masu Sharar Titi Sun Magantu Kan Albashin da Ake Biyansu

 

Wasu mata da aka dauka aikin shara da tsaftace tituna sun ba da labarin rayuwarsu.

Sun bayyana gwagwarmayar da suke sha wajen rayuwa a kan albashin N8000 duk wata.

Matan sun kuma magantu game da shirin, wanda aka tanade shi don inganta rayuwarsu amma hakan bai taimake su da komai ba.

Mata da dama daga Jos, babban birnin jihar Filato sun ba da labarin yadda suke rayuwa a matsayin masu sharar titi don tsaftace titunan jiharsu duk wata saboda albashin N8000.

Matan wadanda mazajensu suka mutu sun bayyana cewa an dauke su aikin ne saboda masu daukar nauyinsu, mazajensu, sun bar duniya kuma yanzu su ke daukar dawainiyar kansu da na yaransu ba tare da taimakon kowa ba, Daily Trust ta rahoto.

Daya daga cikin masu sharar ta ce:

“Ina cikin ma’aikatan farko na ma’aikatar. Gwamnatin Jonah Jang ce ta dauke mu aiki, kuma albashinmu N8000 duk wata. Sun ce suna taimaka mana ne, amma a wasu watannin, basa biyanmu. Ina aikin ne saboda bani da kowa da zai kula da ni. Ina da yara biyar amma biyu sun mutu bayan rasuwar mahaifina. Sauran ukun basu da aikin yi. Saboda haka dole na yi wani abun don kula da kaina.”

An dauki wadanda mazajensu suka mutu aiki don dogaro da kai Matan, wadanda yawancinsu tsoffi ne kuma wasu lokutan sukan yi fama da rashin lafiya, sun ce albashin wata-watan baya taimaka masu wajen ciyar da kansu ko iyalinsu.

Wata mata da ke share titin Rububa a Jos ta ce:

“Matsalata shine cewa wannan N8000 din ba zai iya siyan komai ba. Bana kallon shi a matsayin taimakon gwamnati garemu; kawai dai muna aikin don mu ci abinci ne. Muna ta sa ran gwamnati za ta kara mana albashi, amma sun ki, kuma babu abun da za mu iya yi a kai.”

Manufar daukar wadanda mazajensu suka mutu aikin sharar titi shine don rage talauci wanda gwamnatin tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang ta fara a 2007.

Koda dai gwamnati mai ci ta kara albashin daga N8000 zuwa N33,000 a 2022, matan sun ce ba a aiwatar da shi ba. Yanzu haka, suna bin albashin watanni biyu da tsohon abun da ake biyansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here