Sharhi Barista Nura Ahmad Bayan Gabatar da Shirin HASKEN MATASA Akan Rashin Tsaro

A cikin Shirin HASKEN MATASA Wanda Gidauniyar Aminu Magashi Garba ke daukar nauyi Shirin a duk ranar laraba a tashar Express Radio da misalin karfe 4:30 na yamma, inda Shugaban Kungiyar Mufarka Youth Development initiative, inda ya bayyana yadda matsalar tsaro ke cigaba da adabar al’umma da Kuma rawar da matasa zasu taka wajen magance wanna matsalar, hakazalika Kira ga mahukunta a shafin sa na Facebook.

Barista Nura ya wallafa cewa “A tattaunawarmu ta cikin shirin Hasken Matasa a yammacin yau, mun tattauna halin rashin tsaro da Kasarnan ke ciki da kuma hanyoyin da matasa zasu bunkasa zaman lafiya a unguwanninsu da garuruwansu. Ina daga cikin bakin da shirin ya tattauna da su yau kuma na bada shawarwari kamar haka:

1. Na farko dai duk wani shiri da za’a yi na samar da tsaro da bunkasa zaman lafiya a saka matasa a cikin shirin kuma a basu dama su bayyana ra’ayinsu akan shirin tun daga yadda za’a tsara shi da kuma aiwatar da shi. Domin a lokuta da dama mantawa ake da matasan idan ana gudanar da irin wa wadannan shirye shirye wanda kuma a gaskiyar lamari batun rashin tsaro ko samar da shi su abun yafi shafa.

2. A koda yaushe matsalar tsaro a al’umma tana da alakane da irin matasan da wannan al’umma take dasu. Iya dai dai yawan nagartattun matasan da al’umma take shi, iya dai dai tsaro da zaman lafiyar da zata samu. Kuma ana auna nagartarne da yawan matasan da suke da ilimi, suke da sana’a, sannan kuma da karancin talauci a tsakanin matasan. Wannan shine ma’aunin farko na gano yadda matsayin Kasa yake dangane da tsaro da zaman lafiya.

3. Yawanci irin ayyukan da gwamntoci suke yi na maganta rashin tsaro a Nijeriya shafar kan abun kawai ake yi. Amman ba’a damu da jijjigo tushen matsalar ba; kamar ilmantar da matasa Birni da Karkara, mace ko namiji, samar da abubuwan more rayuwa Birni da Karkara, samar da tsarin kulawa da iyali tsararre daga hukuma kuma a tabbata kowa yana bin wannan tsari.

4. Sannan yana da kyau suma matasa su dafawa gwamnati wajen kokarinta na bunkasa zaman lafiya. Ta yaya za suyi hakan kuwa shine; da farko dai irin Kungiyoyin da muke kafawa a unguwanninmu da garuruwan sai mu tabbatar cewa tsaron unguwannin namu da garuruwanmu yana daga cikin ayyukan da Kungiyar zata yi kuma ayi wani kyakykyawan tsari akan hakan, al’ummar unguwar kuma su tallafawa tsarin wajen aiwatar da shi.

5. Abu na karshe a shawarwarin dana bayar shine wato tun daga lokacin zabe mu daddale da wadanda zamu zaba akan wane tanadi suka yiwa harkokin tsaro kuma mu bibiya muga sun aiwatar da hakan idan an zabe su. Mukan iya zuwa musu da wani tsari ma da muke ganin shine mafita a lokacin da suke yakin neman zabe, mu tallata musu shi don su karba suyi aiki da shi. Haka zalika muma zamu iya takarar zaben idan an zabe mu sai muyi kokari mu gwada wadannan tsare tsare muga ko Allah zaisa a dace.

Ana gabatar da wannan shirine a gidan Rediyon Express ranar kowace Laraba da misalin karfe 4:30 na yamma. Zainab Naseer Ahmad itace shugaban wannan shiri da Kungiyoyin YOSPIS da CHR ke daukar nauyi tare da tallafin Gidauniyyar Aminu Magashi Garba.

Mu huta lafiya!

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here