Kashe ɗalibin Italiya: Ana Shari’ar Jami’an tsaron Masar 
A yau ake ci gaba da shari’ar wasu jami’an tsaron Masar guda hudu, a gaban wata kotu a kasar Italiya.
Ana zargin mutanen da za a yi shari’ar ba tare da su ba, da kashe wani dalibi ɗan kasar Italiya a Alkahira cikin shekarar 2016.
Ana zargin cewa an kashe Guilio Regini, wanda dalibi ne bisa tunanin cewa dan leken asirin kasar waje ne.
Masu gabatar da kara na Italiya sun ce an sace shi ne, kana aka azabtar da shi, daga bisani kuma aka kashe shi.
An tsinci gawarsa da tarin shatin yanka, a wani rami kusa da Alkahira.
Hukumomin Masar sun yi watsi da zargin tare da hana binciken Italiya, lamarin da ya haifar da rikicin diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.
Babu tabbas ko jami’an Masar suna sane da cewa ana gudanar da shari’ar.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here