Za’a Fara Shari’a da Likitocin Tsohon ‘Dan Kwallon Duniya, Maradona Kan Mutuwarsa

 

Ma’aikatan lafiya takwas za su gurfana gaban kotu da laifin sakaci kan mutuwar tsohon dan kwallon duniya Diego Maradona.

Maradona ya mutu a watan Nuwamban 2020 a gidansa dake Buenos Aires, sakamakon bugun zuciya yana da shekaru 60.

Kafin mutuwarsa ya yi jinya bayan an yi masa tiyata a farkon watan da ya rasu.

Sai dai yan kwanaki bayan mutuwarsa ne masu shigar da kara suka kaddamar da binciken likitoci da sauran ma’aikatan lafiyar da suka yi jinyarsa.

Kuma a bara ne suka bada rahoton cewa akwai sakaci da rashin kwarewa ga wasu daga cikin ma’aikatan lafiyar da suka yi jinyar tasa.

Idan aka kama su da laifi a mutuwar tsohon dan kwallon na Argentina, za su iya fuskantar daurin shekaru 25 a gidan yari, kamar yadda kundin sharia a kasar ya tana da.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here