Shari’ar Cin Bashi da Gwamnatin Kano Zata Ci wo

 

Gwamnatin Kano ta na so ta karbo aron kudi daga bankin EXIM a Sin.

Za a yi amfani da wannan kudi ne domin aikin jirgin kasa a cikin gari.

Wasu manya sun nufi kotu, sun nemi Alkali ya hana a ci wannan bashi.

A ranar Talata, wani babban kotun tarayya da ke zama a garin Kano ya bayyana lokacin da zaa saurari karar da aka shigar da gwamnatin Kano.

Wasu sun shigar da gwamna Abdullahi Ganduje kara, su na so a hana shi karbo bashin Naira biliyan 300 daga kasar Sin domin aikin jirgin kasa.

Wata cibiya da ake kira The Centre for Awareness on Justice and Accountability da Kabiru Dakata, sun roki Alkali ya hana karbo wannan bashi.

Wadanda ake tuhuma su ne: gwamnatin jihar Kano, shugaban majalisar tarayya, Ahmad Lawan, majalisar dokokin Kano, sai kuma babban bankin CBN.

Sauran wadanda ake karan su ne: Ma’aikatar kudi, ofishin DMO mai kula da bashi, Bankin EXIM na kasar Sin da kuma ofishin jakadancin kasar a Abuja.

A zaman da aka yi a ranar 29 ga watan Disamba, 2020, an tsaida magana cewa za a koma kotu a ji halaccin karbo wannan kudi N300bn, ko akasin hakan.

Alkali mai shari’a S. I Mark ya bukaci wadanda ake kara su yi wa kotu bayanin abinda ya sa ba za a hana su cigaba da wannan yarjejeniya na cin bashi ba.

A zaman makon nan, kotu ta amince da rokon da wannan kungiya ta ke yi, na mika takardun karar a jakadancin kasar Sin na Najeriya da ke Abuja.

Nan da kusan watanni biyu ake sa ran Alkali ya fara yanke hukunci kan batun wannan bashin.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here