Tsohon Ministan Buhari ya Shawarci Matasa Kan Shirin Shiga Zanga–Zanga
Tsohon Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari ya ba wa ma su shirin zanga-zanga shawarwari a kan illar yin haka ga zaman lafiya.
Sunday Dare, wanda shi ne tsohon Ministan wasanni da ci gaban matasa ya ce har yanzu jama’a ba su gama farfado wa daga zanga-zangar EndSARS ba.
Ya ce akwai fargabar bata-gari za su iya shiga rigar ma su zanga-zanga wajen kawo tashe-tashen hankula a kasa baki daya.
FCT, Abuja – Tsohon Ministan wasanni da ci gaban matasa a gwamnatin Buhari, Sunday Dare ya shawarci matasan kasar nan a kan hanyar samun saukin halin da ake ciki.
Tsohon Ministan ya ce akwai wata hanya da za a bi a maimakon a tafi zanga-zangar gama gari da aka shirya za a yi na kwanaki 15.
Read Also:
A wata hira da tsohon Ministan ya yi ta shafinsa na X, ya ce har yanzu jama’a na kokarin farfado wa daga cikin halin da zanga-zangar endSARS ya ya jefa ‘yan Najeriya.
Akwai fargabar shiga bata-gari zanga-zanga
Tsohon Minista a gwamnatin Buhari, Sunday Dare ya gargadi matasa kan illar da zai iya biyon bayan zanga-zangar gama gari.
The Cable ta wallafa cewa Mista Dare ya ce akwai fargabar bata-gari za su iya shiga rigar masu zanga-zanga wajen tayar da hatsaniya a kasar nan.
Zanga-zanga: Tsohon Minista ya nemi a tattauna
Tsohon Ministan wasanni da ci gaban matasa, Sunday Dare ya bayyana cewa kamata ya yi matasan kasar nan su zauna da gwamnati domin neman mafita.
Ya ce kamata ya yi a zauna, a tattauna da gwamnati a kan hanyar da ta fi dace wa wajen magance koken ‘yan kasa.