Malam Ibrahim Shekarau ya yi Martani Kan Sauke Shugabannin Tsaro
Yan majalisar dattawan Najeriya sun bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sallami hafsoshin tsaro.
Tsohon gwamnan jihar Kano ya jaddada wannan bukata na yan majalisan.
Ya ce ko ba dan rashin kokari ba, bai kamata a cigaba da ajiye hafsoshin tsaron.
ba Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari na karya doka idan ya cigaba da tuburewa kan kin sallaman hafsoshin tsaron Najeriya.
Sakamakon kisan manoma a Zabarmari na jihar Borno, yan Najeriya sun jaddada kira ga sauke hafsoshin tsaro saboda wadanda ke kai yanzu sun gaza.
Read Also:
Shekarau wanda yayi magana a shirin Sunrise Daily na tashar Channels, ya ce ban da maganan gazawarsu, Sojoji sun zarce shekarun da ya kamata suyi, kuma ana saba doka idan suka cigaba da zama.
“Shugaban kasa na karya doka, doka ta ce idan mutum ya kai shekara 60 ya tafi, haka yake,” Yace.
“Idan ka kai shekaru 35 a ofis, wajibi ne ka tafi. Kai, ba ma’aikatan shugaban kasa bane, ma’aikatan gwamnatin Najeriya ne kuma akwai doka.”
Tsohon gwamnan jihar Kanon ya ce shi a ra’ayinsa kawai a bi doka kuma wajibi ne fadar shugaban kasa ta dau mataki.
Shekarau yace cikin dukkansu, babu wanda wa’adinsa bai kare ba ko ya kai shekara 60 ba.