Cire Sashen Jiki: Shekarun Matashin da Sanata Ekweremadu ya Kai Birtaniya
Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya (Nigeria Immigration Service (NIS)) ta ce matashin nan da ake zargin tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan kasar da matarsa Ike Ekweremadu sun kai Birtaniya domin a cire masa koda ba yaro ba ne.
Ranar Lahadi shugaban hukumar driss Jerre ya bayyana cewa takardar haihuwar matashin, David Ukpo, da kuma lambarsa ta dan kasa wato National Identity Number da aka gabatar musu lokacin da za a yi masa fasfo sun cewa shekarunsa 21 ba 15 ba, kamar yadda ake cewa.
Read Also:
“Lokacin da aka yi tattaunawa da shi domin yin fasfo dinsa ranar 2 ga watan Nuwamba, 2021, ya gabatar da da takardar ranar haihuwarsa wadda hukumar kidaya ta kasa ta tabbatar. Ta nuna cewa an haife shi ranar 12 ga watan Oktoba, 2000. Don Allah ku daina yin kalaman da za su zubar da mutuncin hukumar nan,” in ji Jerre, a rokon da ya yi wa ‘yan jarida yayin taron manema labarai.
A ranar Alhamis da ta gabata aka kama tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan, Ike Ekweremadu da matarsa, Beatrice Ekweremadu a Ingila, bisa zargin kai yaron da shekarunsa ba su kai 18 ba kasar domin a cire wani sashe na jikinsa a yi amfani da shi.
Kotun da aka gurfanar da Ekweremadu da matarsa ta bayar da umarnin ci gaba da tsare su har zuwa ranar bakwai ga watan gobe, wato Yuli, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.
Hukumomin ‘yan sandan Birtaniya dai sun ce shekarar matashin 15, wanda hakan ke nuna cewa ana daukarsa a matsayin yaro wanda bai kai munzalin baligi ba.
Hakan na nufin ba za a dauke shi ya isa ya yanke wa kansa shawara ba, wanda hakan ba karamin laifi ba ne a kan duk wani abu da ake zargin an yi masa, da zai kasance kamar ci da guminsa ne.