Jami’ar Abuja na Cikin Cibiyoyin da ke Gudanar da Bada Guraben Shiga ba Bisa Ka’ida ba – JAMB

 

Hadaddiyar Hukumar Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) ta bankado badakalar bada kofofin shiga a jami’ar Abuja.

Hukumar ta ce, an ba ta amince da ba da gurabn shiga irin yadda jami’ar ta Abuja ke gudanarwa ba.

Hakazalika ta shawarci dalibai da su gujewa irin wadannan rashin bin ka’ida da ke faruwa Hadaddiyar Hukumar Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) ta sanya Jami’ar Abuja (UniAbuja) a cikin cibiyoyin da ke gudanar da bada guraben shiga ba bisa ka’ida ba.

A wata sanarwa, Shugaban, Hulda da Jama’a na JAMB, Fabian Benjamin a ranar 13 ga watan Afrilu, ya ce jami’ar na daga cikin cibiyoyin da ke ba da guraben shiga ga dalibai ba tare da sanin hukumar ba.

Ya ce: “Sakamakon haka, irin wadannan guraben shiga sun saba doka, ba za a karbesu ba kuma ya saba wa dokoki da ka’idoji da ke jagorantar shiga manyan makarantu a Najeriya kamar yadda Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta amince kuma aka bayar a CAPS.”

Bugu da kari, kakakin na JAMB, kamar yadda TheCable ta ruwaito, ya ce jami’ar ta kuma bukaci dalibai su biya kudin karbar guraben shigar.

Dangane da abin da ya gabata, Biliyaminu ya shawarci dalibai da kar su yarda ko su biya irin wannan kudaden karbar guraben shigar ko kuma duk wanda CAPS ba ta sarrafa shi ba.

A kalaman nasa yace: “Don haka, Hadaddiyar Hukumar Jarrabawar Shiga Jami’a, tana shawartar dukkan dalibai da kar su yarda da duk wani gurbin shiga da ba a bayar da shi a CAPS ba.

“An shawarci daliban, cikin muradin kansu, kar su yarda da irin wannan da aka yi a waje da jarabawar JAMB ko kuma su biya ko wani irin kudi don karbar gurbin shiga saboda ba za a taba ba da izinin shiga ta irin wannan ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here