Malami ya Shigar da Karar Tsohon Kwamishinan Noma na Nasarawa, Alanana Otaki Kan Zargin Lalata da Matarsa
Ana fafatawa a kotu tsakanin tsohon kwamishanan noma da Malamin jami’a.
Matar Malamin ta bukaci kotu ta raba aurensu da mijinta na shekaru 18.
Malamin yace ya dade yana zargin matarsa na lalata da tsohon kwamishanan.
Lafia, Nasarawa – Mataimakin shugaban kwalejin noma, kimiyya da fasaha dake Lafiya, jahar Nasarawa, Peter Aboki, ya shigar da tsohon kwamishanan noman jahar, Alanana Otaki, kan zargin kwace masa matasa.
Read Also:
A cewar kamfanin dillancin labarai NAN, ita kanta matar Peter Aboki, ya shigar kara kotu inda ta bukaci a tsinke igiyar aurenta da mijinta bayan shekaru 18 suna tare.
Yayin zaman kotun da akayi a garin Lafia ranar Litinin, Lauyan Peter Aboki, Shikama Shyeltu, ya bukaci kotun tayi watsi da karar da matarsa ta shigar na raba auren har sai an kammala shari’ar da ya shigar na zinar da yage zargin tana yi da tsohon kwamishana.
A bangaren lauyan matar David Meshi, ya ce matar tace ita kawai ta gaji da auren kuma hakan yasa ta bukaci a raba su.
Shi kuwa tsohon kwamishanan ta bakin lauyansa, Joseph Agbo, ya ce shi dai bai da hannu a lamarin rikicin auren Peter Aboki da matarsa.
Bayan sauraron dukkan bangarorin, Alkalin kotun Abubakar Lanze, ya dage zaman zuwa ranar 15 ga Satumba, 2021 don cigaba da sauraron karar.