Yau Shugaba Buhari Zai Dawo Daga Landan

 

Ana sa ran dawowar Shugaban kasa Muhammadu Buhari gida Najeriya a yau, Juma’a, 13 ga watan Agusta.

Tuni aka shirya jami’an tsaro a babbar birnin tarayyar domin isowar Shugaban kasar da karfe 5:00 na yamma.

Buhari dai ya je Landan ne domin halartan wani taro na ilimi inda daga nan ya tsaya ganin likitansa.

Landan – Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo Najeriya da karfe 5:00 na yammacin yau Juma’a, 13 ga watan Agusta, bayan kimanin makonni biyu a kasar Ingila.

Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa tuni aka shirya hukumomin tsaro a babban birnin tarayya domin dawowar shugaban.

Shugaban kasar dai ya yi tafiyar ne don halartar taron Ilimi na Duniya kafin ya tsaya domin duba lafiyarsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here