Shugaba Buhari ya Mika Sakon Ta’aziyyarsa ga Tsohuwar Minista,Aisha Abubakar Kan Rashin ‘Danta
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana bakin cikinsa bisa rasuwar Aliyu Abubakar, babban dan tsohuwar minista, Aisha Abubakar.
Matashin Abubakar ya yi hatsarin mota ne tare da ‘yan uwansa su uku da yanzu suke kwance a asibiti.
Shugaban kasar ya bukaci likitoci da sauran ma’aikatan lafiya da ke kula da wadanda hatsarin ya ritsa da su suyi iya kokarinsu.
FCT, Abuja – Tsohuwar karamar ministan Masana’antu, Cinkiyya da Saka Hannun Jari, Aisha Abubakar, ta rasa dan ta, Aliyu Abubakar sakamakon hatsarin mota da ya ritsa da shi, rahoton The Punch.
The Punch ta rawaito cewa yan uwan marigayin uku suma hatsarin ya ritsa da su kuma a halin yanzu suna samun kulawa a asibiti.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyya ga tsohuwar ministan.
Sakon ta’aziyyar Buhari na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar.
Read Also:
A cikin sakon ta’aziyyar da ya aike wa mahaifin marigayin, Kabiru Mukhtar; tsohuwar ministan, wanda hadimansa suka mika, Shugaban kasar ya bayyana rasuwar matashi Aliyu a matsayin abin bakin ciki.
Ya yi wa yan uwansa da suka asibiti a halin yanzu fatan samun sauki cikin gaggawa.
Wani sashi na sakon ya ce:
“Shugaban kasar ya yi wa yan uwan marigayi Aliyu mata biyu da dan uwansa da ke samun kulawa a asibiti addu’ar samun sauki cikin gaggawa.
“Ya bukaci likitoci, malaman jinya da sauran ma’aikatan lafiya da ke kula da su suyi iya kokarinsu don kula da marasa lafiyan.”
Buhari ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan marigayin ya bawa ‘yan uwansa da abokansa hakurin jure rashinsa.
Hadimin Buhari da suka tafi mika sakon ta’aziyyar?
Hadiman shugaban kasar da suka tafi kai sakon ta’aziyyar sun hada da babban mataimakin shugaban kasa na musamman kan ayyuka na musamman, Ya’u Darazo, Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, da Shugaban Tsare-Tsare na Fadar shugaban kasa, Lawal Kazaure.
Ministan ta yi wa shugaban kasa godiya bisa tawagar da ya aika da kuma kauna da kulawa da ya ke nuna musu.