Haƙiƙa babu abin da ya rage illa a yi wa ƴan Nijeriya fatan alheri ga wannan zaɓi da suka yi na shiga ZANGO NA GABA (NEXT LEVEL), na mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.
Fatanmu a nan shi ne ALLAH Ya sa kada a tafka kurakuren da gwamnatin ta yi a baya, na rashin shawo kan matsalar tsaro da ya ƙara taɓarɓarewa a Arewacin ƙasar nan. Gaza farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, gami da gaza daƙile cin hanci da rashawa.
Fatanmu a wannan zango rayuwar talaka ta canja, ya sami abinci sau uku a rana. Ya kwanta idanuwansa duka biyu a rufe. Ya karaɗe ƙasarsa ba tare da fargaba ko tsoron ƴan fashi da makami da garkuwa da mutane a kan tituna ba.
Haƙiƙa hankalin shugaba Buhari ya fi karkata wajen gudanar da wasu ayyukan raya ƙasa ga yankin Yarabawa a shekaru kusan huɗu da suka shuɗe. Wato shiyyar Kudu masu Yamma ( Jihohin Lagos, Ekiti, Osun, Ogun, Ogun da Oyo). Inda ya manta da ainihin shiyyar da ya fito wato Arewa masu Yamma.
Al’ummar yankin na Arewa masu Yamma,su suka fi kowa fama da baƙin talauci da rashin ababen more rayuwa. Duk da haka kuma sune suka zabgawa Shugaba Buhari zunzurutun kuri’u mafi yawa idan an kwatanta da sauran sassan ƙasar. Jihohin wannan shiyyar sune; Kano, Jigawa, Katsina, Sokoto, Zamfara, Kebbi da Kaduna. Wannan yankin ya kamata a ce tun farko an fara bashi kulawa ta musamman a wannan mulki.
A iya cewa gwamnatin Buhari ba ta tsinana musu komai a yankin ba, idan ka kwatanta da abin da sashen Yarabawa wato Kudu masu Yamma suka samu.
Read Also:
Kamar yadda hukumar ƙididdiga ta ƙasa ta tabbatar, jihar Zamfara ita ta fi kowace jiha talakawa a Nijeriya, domin al’ummarta kashi 92% duk talakawa ne. Katsina kuwa kashi 82.2% ne talakawa. Sai Jigawa 88.4%, Kebbi 86% da kuma Sakkwato mai talakawa kashi 85.3 cikin dari. Kano ce mai ɗan sauƙi-sauƙi na kashi 76.9 cikin ɗari.
Su kuwa jihohin da gwamnatin ta mayar da hankali wajen inganta rayuwarsu wato yankin Yarabawa yana cikin yankin da aka sami jihohinsu suna cikin masu ƙarancin talauci domin jihar Osun tana da talakawa kashi 11% ne kacal. Jihar Ondo kuwa kashi 28%. Sai Lagos mai talakawa kashi 8.5%
Wato abin lura anan shi ne duk da mune masu fitowa mu kaɗa ƙuri’u lokacin zaɓe amma kuma mune koma baya wajen sharɓar romon democraɗiyya a gwamnatin Shugaba Buhari. Wato dai abin nan da Bahaushe kan ce ‘kura da shan bugu gardi da amshe kuɗi’.
To wai shin me yasa shugaba Buhari ya yi shakwaliatin ɓangaro da wannnan yankin ? Wai sai yaushe talakan wannan yankin da har yake tsudumawa kwata ya yi wanka don murnar Buhari ya ci zaɓe zai fara sharɓar romon democradoyya ne?
Sai yaushe gwamnatin Buhari za ta samarwa wannan yanki ayyukan raya ƙasa da zai cicciɓasu su fita daga ƙangin fatara da talaucin da suke fama da shi?
Fatanmu a wannan Zango na gaba mu ga an inganta harkokin noma, kasuwanci da masana’antunmu domin mun gaji da ganin kartinmu daga Arewa suna bazama kudancin ƙasar nan domin kawai su yi bara, ko wankin takalmi, tallar tsire, ɗan-kunne da agogo. Ko kuma wasu su zama sune masu gadin Inyamurai da Yarabawa a gidajensu a kudancin ƙasar nan.
Ina ma a ce za a inganta mana Arewarmu don mu daina ganin Bahaushe a tsakiyar kasuwar Ariaria da ke tsakiyar birnin Aba, yana tallar aya ko yalo ko kwakwa? Balanta a ce Hausawa sun daina zama ƴan tura wilbaro domin dakon kayan da Inyamurai ko Yarabawa suka saya a kasuwar Idumeta da ke birnin Iko?
ZAMU CI GABA INSHA ALLAHU
Ado Abdullahi
2-04-2019
The post Shugaba Buhari ya zama inuwar giginya – Ado Abdullahi appeared first on Daily Nigerian Hausa.