Shugaban Mulkin Soji a Sudan, Al-Burhan ya Tsallake Rijiya da Baya
Shugaban rundunar sojin Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kashe shi a wata ziyara da ya kai sansanin soji da ke gabashin kasar.
Read Also:
Janar Burhan yana halartar bikin yaye dalibai a sansanin sojojin na Gibet lokacin da wani harin da jiragen yaki mara matuki suka kai musu. Mutane 5 ne suka mutu yayin lamarin.
Wani mai magana da yawun rundunar wanda ya zanta da BBC ya zargi ‘yan tawayen Rapid Support Forces RSF da hannu a kai harin. RSF ba ta mayar da martani kan zargin ba.
Harin dai shi ne na baya bayan nan a wasu jerin hare-hare da aka kai kan sansanonin sojin da ke kusa da Port Sudan da ke gabar tekun Bahar Maliya.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.